Isa ga babban shafi
wasanni

Serena Williams ta fice daga gasar French Open

Rabon da Serena Williams ta sha kaye hannun Maria Sharapova tun a shekarar 2004.
Rabon da Serena Williams ta sha kaye hannun Maria Sharapova tun a shekarar 2004. REUTERS/Christian Hartmann
Zubin rubutu: Azima Bashir Aminu
1 Minti

Tsohuwar lamba daya a fagen Tennis Serena Williams ta sanar da ficewarta daga gasar French Open yau litinin bayan samun rauni, mintuna kalilan bayan sanar da sunanta zuwa zagaye na hudu inda za ta kara da tsohuwar abokiyar dabinta Maria Sharapova.

Talla

Williams mai shekaru 36 wadda ta lashe kyautar Grand Slam har sau 23 ta ce ta samu raunin ne a kafadarta, ayin karawarta da Julia Goerges a zagaye na uku matakin da ta ce baza ta iya ci gaba da gasar ba.

Sai dai ta ce za ta tsaya duba lafiyarta a birnin Paris idan kuma taga akwai yiwuwar ci gaba da gasar za ta dawo.

Haka zalika Serena Williams ta ki bayar da amsa kan ko za ta kara a gasar Wimbledon da ke tafe nan da makwanni hudu ko a a.

Wannan dai ne karon farko da Williams kea bin kirki tun bayan lashe kyautar Grand Slam a shekarar 2017 yayin gasar Australian Open lokacin tana da tsohon ciki, kuma wannan ce gasa ta uku da ta ke bugawa bayan haihuwarta a bara.

Ko da dai wasu na ganin da gan-gan Williams ta janye daga gasar don gudun shank aye a hannun Sharapova ‘yar Rasha wadda rabonta da yin nasara a hannun Williams tun shekarar 2004.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.