wasanni

Messi ya dara Ronaldo a jerin attajiran 'yan wasa na bana

A jimalace dai Mujallar ta Forbes ta ce baki dayan ‘yan wasan 100 sun mallaki dala biliyan 3 da miliyan 800 daga shekarar da ta gabata zuwa yanzu.
A jimalace dai Mujallar ta Forbes ta ce baki dayan ‘yan wasan 100 sun mallaki dala biliyan 3 da miliyan 800 daga shekarar da ta gabata zuwa yanzu. REUTERS/Juan Medina

Jaridar Forbes ta fitar da sabon jerin sunayen mutane 100 ne da sukafi arziki a duniya, amma fa wannan karon a bangaren masu wasannin motsa jiki, kama daga kwallon kafa, dambe da ma tseren mota.

Talla

Shahararren dan damben boxing na kasar Amurka Floyd Mayweather ya ci gaba da rike kambunsa na mafi kudi a tsakanin masu wasanni na duniya, inda a yanzu ya mallaki arzikin dala miliyan 275.

Cristiano Ronaldo da ya shafe shekaru 2 yana biye da Mayweather a matsayi na 2 a yanzu ya koma na uku, da mallakar arzikin dala miliyan 108, yayinda a yanzu Lionel Messi ya sha gabansa a matsayin na 2 da mallakar dala miliyan 111.

Conor MacGragor dan dambe shi ke a matsayin na hudu a jerin attijaran ‘yan wasan, bayan da ya mallaki dala miliyan 99, sai kuma Neymar dan wasa mafi tsada a duniya na kungiyar PSG a matsayi na 5 a jerin attijiran ‘yan wasan, bayan mallakar dala miliyan 90.

A wanna karon dai babu mace ko daya a tsakanin jerin attajiran ‘yan wasan da Mujallar ta Forbes ta fitar, bayan da a shekarar bara Serena Willaiams 'yar wasan tennis ta bayyana a ciki.

A jimalace dai Mujallar ta Forbes ta ce baki dayan ‘yan wasan 100 sun mallaki dala biliyan 3 da miliyan 800 daga shekarar da ta gabata zuwa yanzu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.