Wasanni

Ronaldo ya amince da biyan tara a maimakon dauri

Cristiano Ronaldo, yayin murnar zura kwallo a ragar Spain, a wasan da aka tashi 3-3 tsakanin Portugal da Spain a gasar cin kofin duniya ta 2018, da ke gudana a Rasha.
Cristiano Ronaldo, yayin murnar zura kwallo a ragar Spain, a wasan da aka tashi 3-3 tsakanin Portugal da Spain a gasar cin kofin duniya ta 2018, da ke gudana a Rasha. PIERRE-PHILIPPE MARCOU / AFP

Gwarzon dan wasan kwallon kafa na duniya, Cristiano Ronaldo, ya amince da biyan gwamnatin Spain tarar euro miliyan 18 da dubu 800, sakamakon aikata laifin kin biyan haraji, a maimakon zaman gidan yari.

Talla

Tun a shekarar da ta gabata ne jami’ai a Spain suka fara tuhumar Ronaldo da kin biyan harajin euro miliyan 14 da dubu 800, zargin da ya musanta.

A watan Yunin shekarar ta bara, dan wasan ya yi tayin biyan gwamnati euro miliyan 14, sai dai gwamnati ta ki amincewa da tayin.

A karkashin dokar hukumar tattara harajin Spain, idan aka yankewa wani ko wata hukuncin daurin shekaru 2 a karon farko, yana da zabin biyan tara, da kuma zama karkashin hukuncin a bisa tsarin daurin talala, amma ba tare da an tsare mai laifin ko kuma saka masa shamakin yin tafiya duk inda ya so ba.

A dai shekarar ta 2017, abokin hamayyar Ronaldo Lionel Messi ya fuskanci hukuncin daurin watanni 21, amma dokar Spain ta bashi damar biyan tara, a maimakon zaman gidan yari.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.