Isa ga babban shafi
wasanni

An sauya mutum-mutumin Ronaldo a Portugal

Musanya mutum-mutumin na zuwa ne sa'o'i kalilan bayan Ronaldon ya zura kwallo ga kasar sa yayin wasan da ya gudana tsakaninsu da Spain.
Musanya mutum-mutumin na zuwa ne sa'o'i kalilan bayan Ronaldon ya zura kwallo ga kasar sa yayin wasan da ya gudana tsakaninsu da Spain. reuters
Zubin rubutu: Azima Bashir Aminu
Minti 1

Hukumomi a Portugal sun musanya mutun-mutumin zakaran kwallon kasar Cristiano Ronaldo da wani sabo wanda ke dauke da sunanshi a filin jirgin saman Madeira.Sauya mutum-mutumin na zuwa ne sa’o’I kalilan bayan zakaran kwallon duniyar ya zurawa kasar tasa kwallo a wasan da suka buga da Spain a Rasha.

Talla

A shekarar 2013 ne dai aka sanya mutum-mutumin aka kuma sauya wani a 2014.

Rahotanni sun ce akwai gagarumin sauyi tsakanin tsohon mutum-mutumin da kuma sabon, inda yanzu wannan aka yi shi yana murumushi sabanin wancan na farko da ya murtuke fuska.

A baya dai mutum mutumin na Ronaldo ya fuskanci suka inda wasu ke kallonsa a matsayin cin fuska maimakon girmamawa.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.