Senegal - Wasanni

Senegal ce kasa ta farko a Afrika da ta yi nasara a gasar cin kofin duniya

Kwallayen biyu a ragar Poland ya bai wa Senegal damar kafa tarihi a matsayin kasar Afrika ta farko da ta yi nasara a wasannin zagayen farko na gasar cin kofin duniya.
Kwallayen biyu a ragar Poland ya bai wa Senegal damar kafa tarihi a matsayin kasar Afrika ta farko da ta yi nasara a wasannin zagayen farko na gasar cin kofin duniya. KHALED DESOUKI / AFP

A yayin da ake gab da karkare zagaye na farko na gasar cin kofin duniya tsakanin kasashe 32 da suka fafata a rukuni takwas na gasar, yanzu haka Senegal ta kafa tarihi a gasar cin kofin duniyar bayan da ta zura kwallo biyu a ragar Poland. Senegal din ta zamo kasa ta farko daga Nahiyar Afrika da ta yi nasara a gasar ta wannan karon.

Talla

Wannan dai ne karon farko da Senegal ta hadu da Poland a tarihin kwallon kafa  kuma dama Senegal din na matsayin babbar abar tsoro a Afrika ta fuskar kwallon kafa, ko da dai itama Poland din ta yi nasara a kusan dukkanin wasannin da ta kara gabanin gasar cin kofin duniya.

Senegal din ta zura kwallo guda a ragar Poland a minti na 34 da fara wasa yayinda ta kara na biyu a minti na 60 kafin daga bisani Poland din ta farke a minti na 86.

Senegal dai ta kafa tarihi ta hanyar zura kwallayen biyu kasancewar babu wata kasa daga nahiyar Afrika da ta taba fara zura kwallo a gasar cin kofin duniyar ta bana, haka zalika ita ce kasa ta biyu daga Afrika da ta zura kwallo a kaf wasannin zagayen farko da ake gab da karkarewa yau, bayan Tunisia da ta zura kwallo guda a ragar Ingila jiya.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.