Wasanni

Masoya na ci gaba da yi wa 'yan wasan Senegal jinjina

'Yan wasan Senegal da magoya bayansu, yayin da suke murnar samun nasara akan  Poland a filin wasa na Spartakda ke birnin Moscow.
'Yan wasan Senegal da magoya bayansu, yayin da suke murnar samun nasara akan Poland a filin wasa na Spartakda ke birnin Moscow. Francisco Leong /AFP

Masoya kwallon kafar kasashen Afrika daga sassan duniya na ci gaba da jinjina wa bajintar da ‘yan wasan Senegal suka yi, a wasan da suka samu nasara kan Poland da kwallaye 2-1, inda suke cewa ba shakka Senegal da fidda nahiyar Afrika kunya a gasar cin kofin duniyar ta bana.

Talla

Kafin wasan na ranar Talata, Senegal ce mai wakiltar nahiyar Afrika daga cikin kasashe 5, da ba a samu nasara akanta ba, a gasar cin kofin duniya da ke gudana bana a Rasha.

Da dama daga cikin magoya bayan dai sun bukaci Super Eagles na Najeriya da su yi koyi da takwarorinsu na Senegal wajen fidda magoya bayansu kunya.

A ranar Lahadi mai zuwa Senegal za ta fafata da kasar Japan, wadda ke jagorantar rukuninsu na 8 bayan lallasa Colombia da 2-1, yayinda ita kuma Poland za ta fafata da Colombia.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.