Wasanni

Argentina ta sha kaye a hannun Crotia da ci 3 mai ban haushi

Tun kafin rashin nasarar ta yau Messi ya sha kakkausar suka daga hannun fitattun 'yan wasan kasar ta sa irinsu Diego Maradona wanda ya gwada misali da yadda Messin ya yi rashin nasara a hannun Jamus a wasan karshe na gasar cin kofin duniya da ya gabata a 2
Tun kafin rashin nasarar ta yau Messi ya sha kakkausar suka daga hannun fitattun 'yan wasan kasar ta sa irinsu Diego Maradona wanda ya gwada misali da yadda Messin ya yi rashin nasara a hannun Jamus a wasan karshe na gasar cin kofin duniya da ya gabata a 2 AFP

Argentina ta sha kaye a hannun Croatia da ci 3 da nema a wasan da ya gudana yau tsakaninsu a zagaye na biyu na gasar cin kofin duniya a Rasha. Nasarar ta Croatia na zuwa a dai dai lokacin da Lionel Messi ke ci gaba da shan suka kan rashin tabuka abin kirki a gasar.

Talla

Ante Rebic ne ya zura kwallon fargo a ragar ta Argentina a minti na 53 da fara wasa bayan dawowa daga hutun rabin lokaci, sai kuma Luka Modric wanda ya zura kwallo na biyu a minti na 80 yayinda Ivanka Rakitic ya zura kwallo na 3 a minti na 91 gab da karkarewa.

Yanzu haka dai Modric shima ya kafa tarihin zura kwallo guda-guda a dukkanin wasanni biyu da kasarsa ta doka a wasannin gasar cin kofin duniyar.

Tun kafin rashin nasarar ta yau Messi ya sha kakkausar suka daga hannun fitattun 'yan wasan kasar ta sa irinsu Diego Maradona wanda ya gwada misali da yadda Messin ya yi rashin nasara a hannun Jamus a wasan karshe na gasar cin kofin duniya da ya gabata a 2014.

Maradona ya ce akwai alamun Messin na neman maimaita abin daya faru a 2014 musamman bayan da ya gaza zura kwallo a bugun daga kai sai mai tsaron gida da aka bashi gab da kammala wasan da suka yi canjaras da Icelan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.