Wasanni

Akwai yiwuwar Ronaldo ya koma Juventus

Shugaban Real Madrid Florentino Perez ya gaza cimma muradin na wasan na biyan yuro miliyan 30 a kowacce kakar wasa, maimakon haka Club din ya bukaci ya biya shi yuro miliyan 25 a kowacce kakar wasa.
Shugaban Real Madrid Florentino Perez ya gaza cimma muradin na wasan na biyan yuro miliyan 30 a kowacce kakar wasa, maimakon haka Club din ya bukaci ya biya shi yuro miliyan 25 a kowacce kakar wasa. REUTERS/Christian Hartmann

Akwai yiwuwar dan wasan gaba na Real Madrid Cristiano Ronaldo ya sauya sheka daga kungiyar zuwa Juventus cikin wannan kaka, bayanda shugaban Real Madrid Florentino Perez ya gaza cimma muradin na wasan na biyan yuro miliyan 30 a kowacce kakar wasa, maimakon haka Club din ya bukaci ya biya shi yuro miliyan 25 a kowacce kakar wasa.

Talla

Ronaldo wanda ke hutu a yanzu haka bayan koro kasarsa daga gasar cin kofin duniya, yaki rattaba hannu kan sabon kwantiragi da Real Madrid amma kuma kawo yanzu babu Club din da ya miko bukatar sayenshi.

Kusan dai hakan ne ya faru da dan wasa a kakar da ta gabata, inda har aka kulle kasuwar cinikayyar ‘yan wasa ba a samu Club din da ya nuna bukatar sayenshi ba, duk kuwa da kwarewarsa a fannin na Tamaula, ko da dai akwai tarin kungiyoyi da ke fatan ganin dan wasan ya taka musu leda ciki kuwa har da ita Yuventus din.

Yanzu haka dai dillalin dan was am Jorge Mendes ya yi wata ganawa da shugabancin na Yuventus game da makomar dan wasan, matakin da ake ganin zai yiwa magoya bayan Juventus din dadi la’akari da lokacin da suka shafe suna fatan sayen dan wasan.

A bangaren Juventus din dai biyan adadin kudaden da Ronaldon ke bukata baa bin damuwa ba ne domin kuwa tuni suka ware yuro miliyan dubu guda don cinikayyar ‘yan wasa a wannan karon, ko da dai ana ganin ba lallai Madrid din ta amince ba, la’akari da cewa yana da sauran kwantiraginsa da Real din zuwa nan da 2021.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.