Wasanni

Faransa ta fitar da Uruguay daga gasar cin kofin duniya

Dan wasan Faransa Raphaël Varane yayin murnar zura kwallon farko a ragar Uruguay, a wasan zagayen gaf da na kusa da  karshe da Faransar ta lallasa Uruguay da kwallaye 2-0.
Dan wasan Faransa Raphaël Varane yayin murnar zura kwallon farko a ragar Uruguay, a wasan zagayen gaf da na kusa da karshe da Faransar ta lallasa Uruguay da kwallaye 2-0. REUTERS/Damir Sagolj

Kwallayen da Varane hadi da Griezman suka jefa a ragar Uruguay sun bai wa Faransa nasarar samun kai wa ga zagayen wasan kusa da na karshe na gasar cin kofin duniya da ke gudana a Rasha.

Talla

Karo na farko kenan da Faransa ta samu nasara wajen kai wa matakin kusa da na karshe a gasar ta cin kofin duniya tun bayan shekarar 2006.

A nata bangaren kuwa, wannan rashin nasara da kasar Uruguay ta yi, ita ce ta farko da ta fuskanta, a dukkanin wasannin da ta buga na gasar cin kofin duniya ta bana da Rasha ke karbar bakunci.

A halin yanzu Faransa za ta yi dakon wanda zai yi nasara a tsakanin Brazil da Belgium, domin fafatawa da shi a zagayen kusa da na karshe a filin wasa da ke birnin Saint Petersburg ranar Talata mai zuwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.