Wasanni

An kammala cinikin Ronaldo zuwa Juventus

Tuni dai Christiano Ronaldo ya wallafa sakon tafiyar ta sa, inda ya ce lokaci ya yi da zai fara sabuwar rayuwa.
Tuni dai Christiano Ronaldo ya wallafa sakon tafiyar ta sa, inda ya ce lokaci ya yi da zai fara sabuwar rayuwa. REUTERS/Christian Hartmann

Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta tabbatar da kammaluwar cinikin Cristiano Ronaldo zuwa Juventus.A dazu da safe ne dai aka ga shugaban kungiyar kwallon kafa ta Juventus Andrea Agnelli ya kai ziyara masaukin Cristiano Ronaldo da ke birnin Kalamata a kudancin Girka.

Talla

Babu tabbacin abin da suka tattauna tsakaninsu yayinda bayan sa’o’I kalilan bangarorin biyu suka sanar da kammaluwar cinikin.

Tun farko Ronaldon wanda ya lashe kyautar Balon d’Or har sau biyar shi da kansa ya nuna bukatar komawa Juventus din kan Yuro miliyan 88.

Kammaluwar cinikin dai ya kawo karshen shekaru 9 da Ronaldo ya shafe a Real Madrid tun bayan sayo shi daga Manchester United kan Yuro miliyan 80, inda ya zamo mafi zura kwallo a raga a tarihin kungiyar bayan da ya zura mata kwallaye 451.

A iya zamanshi a Madrid, Ronaldo dan Portugal mai shekaru 33 ya dage kofunan Laliga 2 Copa del Rey 2 da na zakarun Turai 4.

Tuni dai Christiano Ronaldo ya wallafa sakon tafiyar ta sa, inda ya ce lokaci ya yi da zai fara sabuwar rayuwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.