Isa ga babban shafi
Wasanni

Nadal zai fafata da Djokovic karo na 52 a gasar Wimbledon

Rafeal Nadal, yayin da yake murnar samun nasara akan Juan Martin Del Potro a zagayen gaf da na kusa da karshe na gasar Wimbledon da ke gudana a London..
Rafeal Nadal, yayin da yake murnar samun nasara akan Juan Martin Del Potro a zagayen gaf da na kusa da karshe na gasar Wimbledon da ke gudana a London.. AFP/Glyn KIRK
Zubin rubutu: Nura Ado Suleiman
1 Minti

Gwarzon dan wasan Tennis lamba daya na duniya Rafeal Nadal dan Spain zai fafata da abokin hamayyarsa Novak Djokovic na kasar Serbia, a zagayen kusa da na karshe na gasar Wimbledon da ke gudana a London.

Talla

Karo na shidda kenan da Nadal ya samu kai wa zagayen kusa da na karshen a gasar tennis ta Wimbledon, bayan da a wasan kwata Final na jiya Laraba, Nadal din ya samu nasara kan Juan Martin Del Potro na Argentina da kwallaye 7-5, 6-7, 4-6, 6-4 da kuma 6-4.

Sai da aka shafe sa’o’i 4 Nadal da Del Potro suna fafatawa kafin Nadal ya samu nasarar da kyar.

Sau 51 aka taba haduwa a wasan na tennis tsakanin Djokovic da Nadal, inda Nadal ya samu nasara sau 25, Djokovic kuma ya samu nasara akan Nadal sau 26.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.