Wasanni

Gasar cin kofin duniya ta bana ce mafi kayatarwa a tarihi - Infantino

Shugaban Rasha Vladimir Putin tare da shugaban FIFA Gianni Infantino, da sauran mukarrabansu a filin wasa na kungiyar FC Krasnodar, da ke kudancin birnin na Krasnodar,  a Russia.
Shugaban Rasha Vladimir Putin tare da shugaban FIFA Gianni Infantino, da sauran mukarrabansu a filin wasa na kungiyar FC Krasnodar, da ke kudancin birnin na Krasnodar, a Russia. Reuters/路透社

Shugaban hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA, Gianni Infantino, yace gasar cin kofin duniya ta bana da Rasha ke karbar bakunci ita ce mafi kayatarwa a tarihi.

Talla

Infantino ya bayyana haka ne, yayin da yake yabawa kwamitin hukumar na FIFA da ya jagoranci shirya gasar cin kofin duniyar, da kuma gwamnatin shugaban Rasha Vladmir Putin da ke karbar bakunci.

Shugaban na FIFA ya kara da yabawa akalan wasa, masu horarwa, da ‘yan wasan da suka fafata a gasar cin kofin duniyar ta bana.

Shugaban na FIFA ya ce gasar cin kofin duniya ta bana ta sauya bahagon tunani da wasu kasashen duniya da dama ke yi akan Rasha, kasancewar bakin da suka halarci kasar domin kallon wasannin gasar ta bana, sun fahimci akwai banbanci tsakanin abubuwa da dama da ake fadi akan Rasha, da kuma abin da idanuwansu suka gane musu.

A ranar 14 ga watan Yuni na 2018, aka fara gasar cin kofin duniya ta bana, wadda kuma za ta kare a ranar 15 ga Yuli na 2018, inda za a fafata wasan karshe tsakanin Faransa da Croatia, a filin wasa na Luzhniki da ke birnin Moscow.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.