wasanni

Macron zai tarbi tawagar kwallon Faransa a Paris

Shugaban Faransa Emmanuel Macron a yayin wasan karshe a gasar cin kofin duniya a Rasha
Shugaban Faransa Emmanuel Macron a yayin wasan karshe a gasar cin kofin duniya a Rasha REUTERS

Shugaban Faransa Emmanuel Macron zai tarbi ‘yan wasan kasar da suka lashe gasar cin kofin duniya bayan sun lallasa Croatia da kwallaye 4-2 a wasan karshe a Rasha.

Talla

Shugaba Macron da ya halarci wasan na karshe a filin wasa na Luzhniki, ya yi ta nuna murnarsa a fili a yayin jefa kwallaye a ragar Croatia.

Macron wanda ya halarci Rasha don karfafa wa ‘yan wasan kasarsa guiwa, ya jike da ruwan sama da aka tafka kamar da bakin-kwarya a yayin gabatar da wannan kofin da kasar ta lashe.

Dubun-dubatan Faransawa sun yi cincirindo a Champ Elysees da ke birnin Paris, in da suka yi ta gudanar da bukukuwa tun a cikin daren jiya, kafin wani lokaci a yau Litinin su jinjina wa ‘yan wasan da za a kewaya da su a cikin motar bas dauke da kofin duniyar.

A karo na biyu kenan da Faransa ke lashe kofin duniya bayan wanda ta dauka a shekarar 1998, shekaru 20 da suka gabata.

Kocin tawagar Faransa, Didier Deschamp ya zamo mutun na uku a tarihi da ya lashe kofin duniya a matsayinsa na koci da kuma a matsayinsa na dan wasa, domin yana cikin ‘yan wasan da suka dauki kofin a shekarar 1998.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.