Wasanni

Baki sun kashe Dala biliyan daya da rabi a Rasha

Gasar cin kofin duniya ta taimakawa Rasha wajen samun karin kudaden shiga.
Gasar cin kofin duniya ta taimakawa Rasha wajen samun karin kudaden shiga. REUTERS/Hannah McKay

Babban bankin kasar Rasha, ya ce masoya kwallon kafa da suka kwarara zuwa cikin kasar daga kasashen ketare a yayin gasar cin kofin duniya sun kashe jimillar kudin da ya kai kimanin Dala biliyan 1 da miliyan 500, kwatankwacin Naira biliyan 539 a cikin kasar.

Talla

Binciken ya nuna cewa, masu kallan wasannin sun kashe kudaden ne a kan Otal-Otal da gidajen abinci, amma mafi akasarin makudan kudaden sun tafi ne wajen sayen kayayyakin da suka shafi wasanni.

Hukumomin Rasha sun ce, kimanin masu kallo daga kasashen ketare, dubu 600 ne suka halarci kallan gasar cin kofin duniyar da kasar ta karbi bakwanci a bana, lamarin da ya taka rawa ainun wajen bunkasa kudaden shigar da sashin bude idanu na kasar ya samu.

Gasar ta bana, ita ce mafi girma da kasar ta karbi bakwanci tun bayan rushewar tarayyar Soviet, in da Rashar ta kashe jimillar Dalar Amurka biliyan 11 wajen karbar bakwancin wasannin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.