Chelsea ta sanya farashin euro miliyan 69 kan Morata

Dan wasan gaba na kungiyar Chelsea Alvaro Morata yayin da yake murnar zura kwallo a ragar kungiyar Stoke City, yayin kakar wasa ta bara.
Dan wasan gaba na kungiyar Chelsea Alvaro Morata yayin da yake murnar zura kwallo a ragar kungiyar Stoke City, yayin kakar wasa ta bara. REUTERS/Andrew Yates

Kungiyar Chelsea ta shaidawa AC Milan cewa tilas ta biya farashin euro miliyan 69, muddin tana bukatar sayen dan wasanta Alvaro Morata.

Talla

Chelsea ta sanar da farashin ne bayan soma tattaunawa da wakilan AC Milan tun a ranar Larabar da ta gabata.

Morata ya sauya sheka daga Real Madrid zuwa Chelsea ne a kakar wasa ta bara, kan kudi euro miliyan 57, dominmaye gurbin dan wasan gaba na kungiyar ta Chelsea, Diego Costa da ya koma Atletico Madrid.

Sai dai Morata ya gaza tabuka abin azo gani, la’akari da cewa, kwallaye 11 kawai ya ci wa kungiyar ta Chelsea a wasannin gasar Premier 31 da ya buga mata.

Tuni dai Chelsea ta fara tuntubar kungiyar Juventus, domin yiwuwar sayen dan wasanta na gaba, Higuain, wanda a kakar wasa ta 2015/2016 ya ci wa kungiyar Napoli kwallaye 36 a wasanni 35 da ya buga mata, kafin sauya sheka zuwa Juventus.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.