Rasha

'Yan Najeriya 75 sun yi layar zana a Rasha

Wasu daga cikin 'yan Najeriya da suka kasa komawa gida daga Rasha saboda karewar guzurinsu.
Wasu daga cikin 'yan Najeriya da suka kasa komawa gida daga Rasha saboda karewar guzurinsu. Miodrag Soric/ Twitter

Mai’aikatar harkokin wajen Najeriya ta ce ‘yan kasar 75 daga cikin 230, da suka kasa baro Rasha zuwa gida, bayan kammala gasar cin kofin duniya sakamakon karewar guzurinsu, sun tsere wa jami’an gwamnatin Najeriya da suka je domin mayar da su gida.

Talla

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Najeriya, Tope Elias, ya ce da fari sun kammala tantance bakidayan ‘yan kasar 230 wadanda suka makale a Rashar, sai dai daga bisani, aka farga cewar 155 ne kawai suka shiga jirgin da ya yi jigilarsu zuwa Abuja.

A baya dai an taba samun wasu ‘yan Najeriya mazauna Rasha da suka garzaya ofishin jakandancin kasar da ke Moscow, don neman a taimaka musu su koma gida, bisa rashin jin dadin zama a kasar.

Wadanda suka nemi taimakon dai sun gamu da yaudarar gungun masu safarar mutane, da suka yi alkawarin sama musu ayyukanyi masu romo a kasar ta Rasha, bayan karbe wa kowanne akalla naira dubu 350,000, a matsayin ladan fito, amma sai suka fuskanci akasin alkawarin da aka yi musu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.