Wasanni

Ibrahimovic ya zura kwallaye uku jere a ragar Orlando

Ibrahimovic wanda ya yi ritaya daga bugawa kasarsa kwallo ya zura kwallaye 15 a wasanni 17 da ya bugawa LA Galaxy.
Ibrahimovic wanda ya yi ritaya daga bugawa kasarsa kwallo ya zura kwallaye 15 a wasanni 17 da ya bugawa LA Galaxy. REUTERS/Eric Gaillard

Tsohon dan wasan gaba na Sweden da ke taka leda a LA Galaxy Zlatan Ibrahimovic ya zura kwallaye 3 a jere karon farko a gasar manyan wasanni ta Amurka, matakin da ya bai wa LA Galaxy damar lallasa Orlando da 4-3 a jiya Lahadi.

Talla

Ibrahimovic dan Sweden mai shekaru 36 ya zura kwallaye 15 a wasanni 17 da ya bugawa Galaxy ciki har da ukun jiya wanda ya zura su bayan minti 24 da dawowa daga hutun rabin lokaci.

Yanzu haka dai kungiyar kwallon kafar ta LA Galaxy na matsayin gagarabadau a wasanni 9 data fafata ba tare da anyi nasara a kanta ba.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.