Wasanni

Kamfanin China ya cika alkawarin maidawa mutane dala miliyan 9

'Yan wasan kwallon kafa na Faransa yayin murnar lashe gasar cin kofin duniya ta shekarar 2018.
'Yan wasan kwallon kafa na Faransa yayin murnar lashe gasar cin kofin duniya ta shekarar 2018. REUTERS/Carl Recine

Wani kamfanin kera kayayyakin amfani a dakunan girke-girke, na kasar China Vatti, ya ce zuwa yanzu ya maidawa kwastomominsa jimillar kudade dala miliyan 9.

Talla

Kamfanin ya ce biyan bashin na tilas bangare na cika alwarin da ya dauka na, maidawa duk wanda ya sayi kayansa kudinsa, muddin Faransa ta samu nasarar lashe gasar cin kofin duniya ta bana da aka kammala a Rasha.

Rahotanni sun tabbatar da cewa, bayan nasarar da Faransa ta samu har yanzu kamfanin na Vatti, bai kammala maidawa kwastomominsa kudadensu ba, inda ake sa ran jimillar kudin da zai bbiya, sai ya zarta dala miliyan 12.

Vatti, wanda aka kafa shi a shekarar 1992, daya ne daga cikin kamfanonin da ke daukar nauyin ‘yan wasan kwallon kafa na Faransa, wanda kuma yayi alkawarin duk wanda ya sayi wasu kayansa na musamman kan gasar cin kofin duniyar zai maida masa kudinsa, muddin Farans ta lashe gasar.

Sai dai yayin zantawa da wata mujallar kasar China, wani wakilin kamfanin na Vatti, Wang Zhaozhao ya ce mayar da makudan kudaden ga jama’a bai zai shafi tattalin arzikinsu ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.