Wasanni

Mafarkina na komawa Madrid ya zama gaskiya- Coutois

Thibaut Courtois.
Thibaut Courtois. REUTERS/Sergio Perez

Thibaut Courtois ya jinjina komawrsa kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid don ci gaba da tsare raga, in da ya ce, mafarkinsa ya zamo gaskiya.

Talla

Courtois mai shekaru 26 ya bayyana haka a yayin gabatar da shi a Santiago Bernabeu, in da ya ce, abin girmamawa ne kasancewa tare da babbar kungiyar kwallon kafa a duniya.

Golan ya koma Real Madrid akan Euro miliyan 35 kamar yadda rahotanni ke cewa, in da zai shafe shekaru shida tare da kungiyar mai rike da kambin gasar zakarun nahiyar Turai.

Courtois ya lashe kyautar gwarzon golan da ya fi fice a gasar cin kofin duniya da aka gudanar a bana a Rasha, in da ya nuna bajinta wajen kare ragar kasarsa ta Belgium.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.