Wasanni

Peter Rufa'i ya soki Ahmed Musa kan komawa Saudiya

Dan wasan Najeriya Ahmed Musa, da ya koma gasar wasanni ta kasar Saudiya.
Dan wasan Najeriya Ahmed Musa, da ya koma gasar wasanni ta kasar Saudiya. Reuters

Tsohon mai tsaron raga na Najeriya Peter Rufa’i ya ce dan wasan gaba na Najeriya, Ahmed Musa ya tafka babban kuskure na yanke shawarar barin gasar Premier ta Ingila zuwa gasar kwallon kafa ta kasar Saudiya.

Talla

Bayan kammala gasar cin kofin duniya ta bana a Rasha, wadda a cikinta Ahmed Musa ya taka rawar gani musamman a wasan da Najeriya ta lallasa Iceland, an zaci dan wasan zai sauya sheka ne daga kungiyarsa ta Leicester zuwa wata babbar kungiya ko kuma akalla ya koma tsohuwar kungiyarsa ta CSKA Moscow, kwatsam sai dan wasan ya koma kungiyar Al-Nassr da ke Saudiya.

Sai dai a cewar Peter Rufa’I Ahmed Musa ya cancanci bugawa shahararrun kungiyoyi ne ba irin wadda ya koma ba, la’akari da bajintar da ya nuna a gasar cin kofin duniya ta 2018 da Rasha ta karbi bakunci.

A gobe Juma’a ake sa ran Ahmed Musa zai isa Birnin Riyadh domin shirin fara haskawa a gasar wasannin kwallon kafar kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.