Wasanni

Rashin kudi ya hana mu daukar hayar Guardiola - Argentina

Hukumar kula da kwallon kafa ta Argentina ta ce ta yi kokarin daukar kocin Manchester City, Pep Guardiola a matsayin mai horar da ‘yan wasanta, amma hakarta ta gaza cinma ruwa, saboda rashin isassun kudade.

Mai horar da kungiyar Manchester City Pep Guardiola.
Mai horar da kungiyar Manchester City Pep Guardiola. Reuters/Hannah Mckay
Talla

Shugaban hukumar kwallon ta Argentina Claudio Tapia, ya ce bayan da suka tuntubi Guardiola kan yiwuwar daukarsa aiki, sun gano muddin suna son bukatarsu ta biya, sai sun bada jinginar ita kanta hukumar kafin samun bashin kudin da za su biya shahararren kocin albashi, wanda shi ma ba lallai bane su isa.

A halin yanzu hukumar kwallon Argentina ta bayyana Mauricio Pochettino mai horar da Tottenham da Diego Simeone a matsayin wadanda za su yi kokarin tattancewa don jagorantar kwallon kafar kasar, amma sai a watan Disamba mai zuwa za su yanke shawara ta karshe.

A watan da ya gabata, Argentina ta sallami mai horar da ‘yan wasanta Jorge Sampaoli, bayan kashin da suka sha a gasar cin kofin duniya da Rasha ta karbi bakunci, inda a yanzu, tsaffin ‘yan wasan kasar Lionel Scaloni da Pablo Aimar suke rikon wucin gadi na horar da ‘yan wasansu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI