Isa ga babban shafi
Wasanni

Bayern Munich ta lallasa Frankfurt da kwallaye 5-0

Robert Lewandowski na kungiyar Bayern Munich.
Robert Lewandowski na kungiyar Bayern Munich. REUTERS/Michaela Rehle
Zubin rubutu: Nura Ado Suleiman
Minti 1

Kungiyar Bayern Munich ta lashe gasar Super Cup ta Jamus bayan da ta lallasa Eintracht FrankFurt da kwallaye 5-0.

Talla

Dan wasan gaba na kungiyar ta Bayern Munich, kuma dan kasar Poland Robert Lewandoski ne ya ci wa kungiyar tasa 3 daga cikin kwallayen biyar da suka jefa a ragar Frankfurt, yayinda Kingsley Coman da Thiago Alcantara suka jefa ragowar kwallaye biyun.

Nasarar da Munich ta samu, a wasan na ranar Lahadi, tamkar ramuwa ce kan wasan karshe na gasar Super Cup din ta Jamus a kakar bara, inda Frankfurt ta doke ta da kwallaye 3-1.

A kwanakin baya dai akwai shakku kan ci gaba da zaman Robert Lewandoski a kungiyar ta Bayern Munich, inda aka rika alakanta dan wasan da sauyin sheka zuwa wasu kungiyoyin nahiyar Turai ciki har da Real Madrid.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.