Isa ga babban shafi
Najeriya

Jami'an tsaron DSS sun tsaurara matakan tsaro a hukumar NFF

Wasu jami'an tsaron hukumar farin kaya ta Najeriya DSS.
Wasu jami'an tsaron hukumar farin kaya ta Najeriya DSS. guardian.ng
Zubin rubutu: Nura Ado Suleiman
2 Minti

A Yau Litinin hukumar jami’an tsaron farin kaya ta Najeriya DSS ta tsaurara matakan tsaro a hedikwatar hukumar lura da wasannin kwallon kafa ta Najeriya NFF da ke garin Abuja, domin tabbatar da doka da oda.

Talla

Matakin ya biyo bayan karewar wa’adin da hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA ta debawa Najeriya, na kawo karshen rikici ko takaddama kan shugabancin hukumar ta NFF da ake ci gaba da samu tsakanin Amaju Pinnick da Chris Giwa.

Rikici kan shugabancin hukumar ta NFF da ya shafe kusan shekaru 4, ya samo asali ne tun a 2014, inda a ranar 26 ga watan Agustan shekarar, wasu wakilan hukumar da NFF suka zabi Amaju Pinnick a matsayin shugabansu a Abuja, yayinda bangaren Chris Giwa suka gudanar da nasu zaben a ranar 30 ga watan Satumba na shekarar ta 2014 a garin Warri.

A baya bayan nan ne dai ranar 2 ga watan Yuli na shekarar 2018 da muke ciki, bangaren Chris Giwa ya karbe harkokin gudanar da hukumar ta FIFA sakamakon hukuncin kotun kolin kasar na ranar 27 ga watan Afrilun 2018, da ya mikawa Giwa shugabancin hukumar ta NFF.

To sai dai lamarin ya sauya daga ranar 13 ga watan Yuli da ya gabata, inda gwamnatin Najeriya ta baiwa jami’an tsaron DSS umarnin maidawa Amaju Pinnick shugabancin hukumar ta NFF, biyo bayan zantawar da shugaban FIFA Ginanni Infantino yayi da ‘yan Jaridu a Rasha, inda ya ce Hukumar ta FIFA bata san wani shugaban NFF da ya wuce Pinnick ba.

A da ake ciki tuni gwamnatin Najeriya ta soma daukar matakan ganin kasar bata fuskanci fushin hukumar FIFA ba na daukar matakin dakatar da ita daga shiga wasannin a matakin nahiya ko duniya.

Bayaga zama da bangarorin da ke rikici da juna bisa shugabancin hukumar kwallon kafar Najeriya NFF, wato Chris Giwa da Amaju Pinnick, an wata majiya ta ce gwamnatin Najeriyar ta aike da wasika zuwa ga FIFA inda ta ke bata tabbacin cewa harkokin wasannin kwallon kafa na ciga da gudana yadda ya kamata bisa tsarinta, zalika Amaju Pinnick da mukarrabansa ke jagorantar hukumar NFF.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.