Isa ga babban shafi
Wasanni

George Weah na fuskantar suka bisa shirinsa na karrama Wenger

Shugaban kasar Liberia, kuma tsohon gwarzon dan wasan kwallon kafa na duniya, George Weah.
Shugaban kasar Liberia, kuma tsohon gwarzon dan wasan kwallon kafa na duniya, George Weah. REUTERS/Thierry Gouegnon
Zubin rubutu: Nura Ado Suleiman
2 min

Shugaban kasar Liberia, kuma tsohon gwarzon dan wasan kwallon kafa na Duniya Goerge Weah na fuskantar suka daga wasu da ke adawa da shirinsa na karrama tsohon mai horar da Arsenal Arsene Wenger da lambar yabo mafi daraja ta kasar Liberia.

Talla

Weah wanda ya dare shugabancin Liberia a shekarar bara, na shirin karamma Arsene Wenger da wani tsohon kocin kasar Faransa Claude Le Roy da lambar yabon Liberia mafi girma ne a gobe Juma’a.

Sai dai daya daga cikin masu adawa da shugaban Na Liberia Darius Dillon, ya ce bai kamata Weah yayi amfani da labar yabon kasar ta Liberia mafi daraja, wajen girmama wadanda suka bashi gudunmawa a raywarsa kadai ba.

Wenger da Claude Le Roy dai sun taka muhimmiyar rawa a nasarar da Goerge Weah ya samu a fagen kwallon kafa

A shekarun 1980 zuwa da 1986 ne Le Roy ya fara gano Weah a lokacin da ya ke bugawa wata karamar kungiya wasa a Kamaru, daga nan ne ya sada dan wasan da Arsene Wenger, a lokacin da horar da kungiyar Monaco, wanda bai bata lokaci be wajen daukar shi a kungiyar tasa.

Bayan kwarewar da ya samu a karkashin Wenger da ke horar da Monaco a waccan lokacin, likkafar George Weah ta kara dagawa, inda ya koma kungiyar PSG, kafin daga bisani ya sauya sheka zuwa kungiyar AC Milan.

Nasarorin da Weah ya samu a kungiyoyin da ya bugawa wasanni, da kuma a matakin kasarsa da ya wakilta ne, ya bashi damar zama dan nahiyar Afrika daya tilo, da ya lashe kyautar hukumar FIFA ta gwarzon dan wasan kwallon kafa na duniya a shekarar 1995.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.