Wasanni

Rabuwa da Real Madrid na cikin matakai mafi sauki a rayuwata - Ronaldo

Cristiano Ronaldo na kungiyar Juventus yayin fafatawa da dan wasan kungiyar Chievo Verona Nicola Rigoni, a gasar Seria A ta Italiya. 18, ga Agusta, 2018.
Cristiano Ronaldo na kungiyar Juventus yayin fafatawa da dan wasan kungiyar Chievo Verona Nicola Rigoni, a gasar Seria A ta Italiya. 18, ga Agusta, 2018. REUTERS/Alberto Lingria

Cristiano Ronaldo ya ce yanke shawarar rabuwa da kungiyar Real Madrid tare da komawa Juventus, na daga cikin matakai mafiya sauki da ya dauka a rayuwarsa.

Talla

Ronaldo mai shekaru 33, ya yi wannan furuci ne a lokacin da yake zantawa da wata kafar yada labarai a Italiya, inda ya bayyana matkar mamakin ganin irin karrama shi da magoya bayan kungiyar Juventus suka yi a Turin.

Bayan shafe shekaru a Spain Ronaldo ya taimakawa Real Madrid samun nasarar lashe kofin gasar zakarun kungiyoyin nahiyar turai 4, kafin daga bisani, ya yanke shawarar rabuwa da kungiyar, ya koma Juventus kan farashin Fam miliyan 105.

A cewar Ronaldo bai taba tunanin zai bugawa Juventus wasa ba, amma sai gashi a kungiyar.

A cewar dan wasan ba shakka ya samu dimbin nasarori a Real Madrid wadanda yake mutuntawa, sai dai a halin yanzu abubuwa ne da suka shude.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.