Wasanni

Ancelotti zai fafata da tsohuwar kungiyar da ya horar

Sabon mai horar da kungiyar Napoli, Carlo Ancelotti zai jagoranci kungiyar buga wasan farko a karkashin jagorancinsa inda zai fafata tsohuwar kungiyarsa da ya horar AC Milan.

Carlo Ancelotti sabon mai horar kungiyar Napoli da ke gasar Seria A na kasar Italiya.
Carlo Ancelotti sabon mai horar kungiyar Napoli da ke gasar Seria A na kasar Italiya. REUTERS/Charles Platiau/File Photo
Talla

A gobe Asabar ne za’a fafata wannan wasa da zai dauki hankula musamman a duniyar wasannin gasar Seria A ta kasar Italiya.

Baya dai Ancelotti ya shafe shekaru 8 yana horar da kungiyar AC Milan daga shekarar 2001 zuwa 2008, wadda a karkashinsa ne ta samu dimbin nasarori tsakanin takwarorinta na nahiyar turai.

Bayan horar da AC Milan, Ancelotti ya koma Chelsea daga watan Yuli na 2009 zuwa Mayu a 2011, sai kuma kungiyar PSG da ya horar da ita tsawon kusan shekaru biyu daga watan Disamba a 2011 zuwa Yuni na 2013.

Daga nan ne Ancelotti ya horar da Real Madrid daga 2013 zuwa 2015 kafin komawa kungiyar Bayern Munich a 2016 kuma ya rabu da su a shekarar.

A watan Mayu na shekararda muke ciki, ya kawo karshen kauracewa gasar Seria A da ya yi tsawon shekaru 9 inda ya karbi jagorancin horar da kungiyar Napoli.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI