Isa ga babban shafi
Wasanni

Tottenham ta kara dagulawa Manchester United lissafi

Kocin Manchester United Jose Mourinho na dada fuskantar matsin lamba.
Kocin Manchester United Jose Mourinho na dada fuskantar matsin lamba. Reuters/Jason Cairnduff
Zubin rubutu: Abdurrahman Gambo Ahmad
Minti 2

Kungiyar Kwallon Kafa ta Tottenham ta ci gaba da samun tagomashi a sabuwar kakar gasar firimiya ta Ingila bayan ta yi nasarar lallasa Manchester United da kwallaye 3-0 a Old Trafford, abin da ya kara matsin lambar da Jose Mourinho ke fuskanta.

Talla

Koci Mourinho ya yi fatan Manchester United za ta murmure daga kashin da ta sha a hannun Brighton a wancan makon da ya gabata, amma Tottenham ta kara dagula mata lissafi.

Tun shekarar 1992-93 rabon da Manchester United ta gamu da mafi munin rashin nasara a farkon kakar gasar firimiya ta Ingila, kuma a karon farko kenan da Mourinho ke shan kashi a wasanni biyu daga cikin uku a farkon gasar ta Lig.

Harry Kane ne ya fara zura kwallon farko a minti na 50 kafin daga bisa Lucas Moura ya zura ta biyu dfa ta uku a minti na 52 da kuma 84.

A bangare guda Mourinho ya bukaci ‘yan jarida da su ba shi girma yayin da ya fice daga taron manema labarai da ya gudana bayan dukan da suka sha a hannun Tottenham.

A cewar Mourinho, shi kadai ya lashe kofin firmiya sau uku fiye da sauran kociyoyi 19, da suka lashe sau biyu kacal, don haka yana ganin ya

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.