Wasanni

Manchester United ta fara farfadowa

Kungiyar Kwallon Kafa ta Manchester United ta fara murmurewa daga rashin karsashi bayan ta yi nasarar doke Burnley da kwallaye 2-0 a gasar firimiyar Ingila duk da cewa dan wasanta Paul Pogba ya barar da bugun fanariti, yayin da aka bai wa Marcus Rashford jan kati. Nasarar Manchester United ta faranta ran kocinta Jose Mourinho wanda ke fuskantar barazanar sallama daga kungiyar.

Kocin Manchester United, Jose Mourinho na fuskantar barazanar sallama daga kungiyar
Kocin Manchester United, Jose Mourinho na fuskantar barazanar sallama daga kungiyar REUTERS/Andrew Yates
Talla

Romelu Lukaku ne ya cire wa Manchester United kiste a wuta, in da ya zura dukkanin kwallayen biyu a minti na 27 da kuma 44, abin da ya fardado da ita daga dukan da ta sha a hannun Brighton da Tottenham a wasannin da suka yi a baya.

Pogba ya samu damar bugun fanariti bayan ketar da Aaron Lennon ya yi wa Rashford, amma mai tsaren ragar Burnley Joe Hart ya tare kwallon.

A bangaren Rashford kuwa, a karon farko kenan da ake bai wa dan wasan jan kati tun bayan da ya fara taka leda.

Wannan nasarar ta bai wa Manchester United damar haurawa zuwa mataki na 10 a teburin gasar ta firimiyar Ingila.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI