Wasanni

Sharhi kan jadawalin gasar zakarun Turai

Sauti 10:10
Tambarin gasar cin kofin zakarun nahiyar Turai
Tambarin gasar cin kofin zakarun nahiyar Turai REUTERS/Jean Pierre Amet

Shirin Duniyar Wasanni na wannan makon tare da Abdurrahman Gambo Ahmad ya yi sharhi ne kan rukunai mafi wahala a  jadawalin gasar cin kofin zakarun Turai ta bana. Kazalika a karon farko kenan cikin shekaru 9 da Real Madrid za ta fafata a gasar ba tare da gwarzon dan kwallon duniya ba, wato Christiano Ronaldo da ya koma Juventus. Har ila yau shirin ya yi nazari kan kalubalen da ke gaban Manchester United da kuma cece-kucen da ake yi kan yadda aka bai wa Luca Modric kyautar gwarzon dan kwallon nahiyar Turai.