Wasanni

Toure ya kammala komawa Olympiakos

Yaya Touré ya koma Olympiakos ta Girka
Yaya Touré ya koma Olympiakos ta Girka AFP PHOTO / OLI SCARFF

Kungiyar kwallon kafa ta Olympiakos ta gabatar da tsohon dan wasan Manchester City, Yaya Toure ga magoya bayanta bayan ya kammala kulla kwantiragi da babbar kungiyar ta Girka.

Talla

Dama dai Toure ya taba taka leda a Olympiakos a can bayan kafin ya raba gari da ita a shekarar 2006, in da ya koma Monaco da Barcelona tsakanin shekarar 2007 zuwa 2010.

Magoya bayan Olympiakos sun nuna farin cikinsu da isowar Toure, dan asalin kasar Cote d’Ivoire kuma mai shekaru 35 a jiya Lahadi, in da suka yi ta kunna wuta tare da kewaye shi.

A karshen kakar da ta gabata ne, dan wasan ya raba gari da Manchester City bayan ya buga ma ta wasanni 230 tare da jefa kwallaye 59.

Sai dai a baya-bayan nan, dan wasan ya koka kan yadda kungiyar ta hana shi damar buga wasanni.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.