Wasanni

NFF ta dakatar da kocin Super Eagles kan cin hanci

Kochin Super Eagles, Salisu Yusuf
Kochin Super Eagles, Salisu Yusuf Goal.com

Kwamitin Da’a na Hukumar Kwallon Kafar Najeriya, NFF ya dakatar da babban kocin tawagar Super Eagles, Salisu Yusuf daga shiga harkokin wasannin kwallo har na tsawon shekara guda tare da cin sa tarar Dala dubu 5.

Talla

Wannan na zuwa ne bayan wani faifen bidiyo ya nuna Kocin na karbar cin hancin Dala dubu 1 daga hannun wani dan jarida da ya bad da kama.

Dan jaridar ya gabatar da kansa a matsayin wakilin ‘yan wasa biyu da suka hada da Osas Okoro da Rabiu Ali, in da ya bada cin hancin don sanya ‘yan wasan cikin jerin sunayen masu wakiltar Najeriya a gasar cin kofin zakarun kasashen Afrika ta 2018 a Morocco.

Koda yake Yusuf ya musanta aika laifi, kuma yana da damar daukaka kara don kalubalantar wannan hukuncin.

A wani labarin daban,  jami’an tsaron sub cafke tsohon shugaban Hukumar Kwallon Kafar Benin, Anjorin Moucharafou kan zargin sace kayayyakin wasanni.

Majiyar shari’a ta bayyana wa Kamfanin Dillancin Labaran Faransa na AFP cewa, an tsare Moucharafou ne a yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike kan batun satar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.