Wasanni-kwallon kafa

Babu tabbacin zan sauya sheka a watan Janairu - Pogba

Pogba wanda kawo yanzu suka gaza sasantawa tsakaninsa da Jose Mourinho ya ce zai fatan jita-jitar da ake ta maye gurbin kociyan da Zinadine Zidane ta tabbata.
Pogba wanda kawo yanzu suka gaza sasantawa tsakaninsa da Jose Mourinho ya ce zai fatan jita-jitar da ake ta maye gurbin kociyan da Zinadine Zidane ta tabbata. REUTERS/Dylan Martinez

Dan wasan Faransa da ke taka leda a Manchester United Paul Pogba ya ce baya tsammanin sauya sheka ko da a kakar cinikayyar ‘yan wasa ta watan Janairu bayan takun sakar da ya ke fuskanta tsakaninsa da kociyan United din Jose Mourinho.

Talla

Kalaman na Pogba dai na zuwa ne a dai dai lokacin da wasu jita-jitar maye gurbin Mourinho da Zinadine Zidane ke ci gaba da ruruwa, wanda dan wasan ya ce zai fi kowa farin ciki da hakan.

Pogba wanda shi ne dan wasan United mafi tsada da ta siya kan Yuro miliyan 89 daga Juventus har yanzu sun gaza sasantawa da Mourinho amma duk da haka ya ce bai ga yiwuwar sauya shekarsa nan kwana kusa ba.

Pogba mai shekaru 25 wanda ya lashe kofin duniya bana, akwai dai rade-radin da ke cewa ya na kokarin komawa Barcelona ko da dai ya musanta hakan, yayinda a bangare guda itama United din ta ki amincewa da tayin na Barcelona a kakar musayar ‘yan wasan da ta gabata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.