Wasanni-kwallon kafa

Ni na cancanci na lashe kyautar Ballon d'Or bana - Griezman

Dan wasan faransa da ke taka leda a Atletico Madrid Antoine Griezman ya yi ikirarin cewa shi ne ya cancanci lashe kyautar zakaran kwallon duniya ta Ballon d’Or a bana.

A cewar Griezman wannan shekarar ta sa ce, domin kuwa za a sanya shi cikin fitattu 3 kafin daga bisani a zabe shi a matsayin zakara a kuma bashi kyautarsa.
A cewar Griezman wannan shekarar ta sa ce, domin kuwa za a sanya shi cikin fitattu 3 kafin daga bisani a zabe shi a matsayin zakara a kuma bashi kyautarsa. REUTERS/Vincent Kessler
Talla

Griezman wanda ya lashe kofin duniya a Rasha bana, ko a shekarar 2016 shi ne yazo na uku a jerin ‘Yan wasan da suka fi nuna bajinta a fagen tamaula ciki har da Cristiano Ronaldo na Portugal da dan wasan Argentina Messi.

A shekarar ta 2016 dai Griezman ya gaza lashe kofin Euro a bangaren faransa da kuma na zakarun Turai a bangaren Atletico.

Sai dai ana ganin a wannan karon ikirarin na Griezman ka iya zama gaskiya la’akari da rawar da ya taka wajen lashe kofin Europa da na UEFA Super Cup a bangaren Atletico da kuma Kofin duniya dungurum.

A cewar Griezman wannan shekarar ta sa ce, domin kuwa za a sanya shi cikin fitattu 3 kafin daga bisani a zabe shi a matsayin zakara a kuma bashi kyautarsa.

A cewar dan wasan wanda yaki amincewa da sauya sheka zuwa Barcelona a wannan kaka, matukar aka ki karramashi da kyautar ta Ballon’d’Or to fa an tasamma rashin adalci ne, domin kuwa tsakanin Ronaldo da Messi wadanda suka shafe shekaru suna lashe kytautar babu wanda ya nuna bajintar da ya nuna.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI