Wasanni

Jamus ta rike Faransa a wasan Nations League

Faransa ce ke rike da kofin duniya da ta lashe a Rasha
Faransa ce ke rike da kofin duniya da ta lashe a Rasha REUTERS/Christian Hartmann

Faransa mai rike da kambin duniya ta tashi wasa ba-kare-bin-damo da Jamus a gasar cin kofin manyan tawagogin kasashen nahiyar Turai ko kuma Nations League da aka fara gudanarwa a karon farko a cikin watan Satumban da muke ciki bayan kammala gasar cin kofin duniya a Rasha.

Talla

A karon farko kenan da Faransa ke buga wasan kasa da kasa tun bayan da ta doke Croatia a wasan karshe a gasar cin kofin duniya a Rasha.

Koda yake kididdiga ta nuna cewa, Jamus ta fi rike kwallo da kashi 60, yayin da Faransa ke da kashi 40.

Kazalika Jamus ta kaddamar da kyawawan hare-haren a raga har sau 6, yayin da Faransa ta kai 4.

Watakila ana iya cewa, Jamus ta fara maido da karsashin da aka santa da shi bayan mummunan kashin da ta sha a gasar cin kofin duniya a Rasha, in da aka yi waje da ita tun a matakin rukuni.

A ranar Lahadi mai zuwa ne, Faransa za ta karbi bakwncin Netherlands a matakin rukuni na biyu na wannan sabuwar gasa.

A bangare guda, kasar Portugal ta rike Croatia 1-1 a wani wasan sada zumunta da kasashen biyu suka yi a Lisbon.

Pepe ne ya farke kwallon da Perisic ya fara zurawa a ragar Portugal.

Dan wasan Portugal da ke taka leda a Juventus, Christiano Ronaldo bai samu damar buga wasan ba bayan ya ce, baya jin dadin jikinsa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.