Wasanni

Williams ta kama hanyar lashe gasar US Open

Serena Williams ta Amurka
Serena Williams ta Amurka Danielle Parhizkaran-USA TODAY SPORTS

Serena Williams ta kama hanyar lashe babbar gasar Tennis a karon farko tun bayan haihuwarta, bayan ta samu nasarar doke Anastasija Sevastova ta Latvia a cikin minti 66 a gasar US Open.

Talla

Williams wadda ta sha kashi a hannun Angelique Kerber a wasan karshe a a gasar Wimbledon a cikin watan Juli, ta samu nasara akan Sevastova ne a matakin wasan dab da na karshe a US Open da ci 6-3 da 6-0

Yanzu haka Williams mai shekaru 36 za ta hadu da Naomi ta Japan a a wasan karshe na gasar US Open a ranar Asabar.

Williams ba ta samu damar buga gasar ba a bara sakamakon fama da laruar bayan haihuwa, yayin da ta bayyana cewa, yanzu da dawo da karsashinta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.