Wasanni

An ci tarar Serena Williams Dala dubu 17

serena Williams ta zargi alkalin wasa da yi mata rashin adalci a wasan karshe a gasar US Open
serena Williams ta zargi alkalin wasa da yi mata rashin adalci a wasan karshe a gasar US Open Danielle Parhizkaran-USA TODAY SPORTS

An ci tarar Serena Williams Dala dubu 17 sakamakon karya dokokin wasan kwallon Tennis a yayin wasan karshe a gasar US Open da ta kashi a hannun Naomi Osaka ta Japan.

Talla

Williams ta zargi alkalin wasa da rashin adalci har ta kira shi makaryaci kuma barawo, lamarin da ya sa ya rage mata makin wasa guda.

Kazalika 'yar wasan ta zargi alkalin da nuna mata wariya domin a cewarta, ba ya daukan mataki akan 'yan wasa maza da ke kiran sa barawo.

Williams ta ki yin musafaha da alkalin wasan bayan kammala fafatawar, abin da ke dada nuna yadda ta kullace shi.

Osaka mai shekaru 20 ta lashe wasan ne da ci 6-2 da 6-4, abin da ya sa ta zama ‘yar asalin Japan ta farko a tarhi da ta lashe babbar gasar kwallon Tennis.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.