Wasanni

Ina son 'yan wasan Liberia su yi koyi da Najeriya- Weah

Shugaban kasar Liberia, kuma tsohon gwarzon dan wasan kwallon kafa na duniya, George Weah.
Shugaban kasar Liberia, kuma tsohon gwarzon dan wasan kwallon kafa na duniya, George Weah. REUTERS/Thierry Gouegnon

Shugaban Liberia kuma tsohon gwarzon dan kwallon duniya George Weah ya ce, Najeriya ta samu ci gaba sosai a fagen tamaula kuma yana bukatar kasarsa ta yi koyi da tawagar Super Eagles.

Talla

Shugaban ya ce, a lokacin da yake matashin dan kwallo, 'yan wasan Najeriya irinsu Stephen Keshi da Rashidi Yekini da Fridya Ekpo da sauransu na burge shi matuka.

Wannan na zuwa ne bayan Weah ya nuna tsoffin dabarunsa a wasan sada zumunta da Najeriya da doke Liberia da kwallaye 2-1 a birnin Monrovia, in da ya buga wasan har tsawon minti 79 kafin a sauya shi ana saura minti 12 a tashi wasan.

A shekarar 1995 ne aka zabi Weah a matsayin gwarzon dan wasan duniya da nahiyar Turai da kuma Afrika.

Tsohon dan wasan wanda ya lashe kujerar shugabancin kasa da gagarumin rinjaye a zaben bara, ya kasance mutun daya tilo daga nahiyar Afrika da ya taba lashe kyautar gwarzon dan kwallon duniya kuma a cewarsa yana fatan nan gaba za a sake samun dan wasan Afrika da zai lashe kyautar ta gwarzon dan wasa a duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.