Wasanni

Terry ya yi watsi da tayin Spartak Moscow

John Terry.
John Terry. REUTERS/Stefan Wermuth

Tsohon kaften din tawagar kwallon kafar Ingila wanda kuma ya taka leda a Chelsea, John Terry ya yi watsi da kwantiragin da Kungiyar Kwallon Kafa ta Spartak Moscow ta Rasha ta yi masa tayi.

Talla

A cewar dan wasan, ya dauki matakin ne bayan nazari tare da iyalinsa kuma suka yanke shawarar cewa, a wannan lokaci ba za su iya barin in da suke ba don komawa Moscow.

Tun lokacin da kwantiraginsa ya kare da Aston Villa a farkon kakar da muke ciki, Terry  ke zama a gida ba tare da aikin taka tamaula ba.

Dan wasan ya buga wa Chelsea wasanni har sau 700 tare da taimaka mata lashe kofuna da dama da suka hada da kofunan firimiya guda biya da kofunan FA biyar da kuma gasar cin kofin zakarun Turai a shekarar 2012.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.