Wasanni

FIFA bata yi min adalci ba - Griezmann

Antoine Griezmann yayin murnar lashe gasar cin kofin duniya ta 2018, bayan kammala wasan karshe da suka lallasa Croatia ta kwallaye 4-2 a filin wasa na Luzhniki da ke birnin Moscow.  15 juillet 2018.
Antoine Griezmann yayin murnar lashe gasar cin kofin duniya ta 2018, bayan kammala wasan karshe da suka lallasa Croatia ta kwallaye 4-2 a filin wasa na Luzhniki da ke birnin Moscow. 15 juillet 2018. REUTERS/Christian Hartmann

Dan wasan gaba na Atletico Madrid, kuma tauraron tawagar kwallon kafar Faransa da ya taimaka mata lashe gasar cin kofin duniya Antoine Griezman, ya ce ya rasa dalilin da ya hana hukumar FIFA sanya shi cikin ‘yan wasa uku wadanda daga cikinsu za ta tantance gwarzon duniya na shekarar bana.

Talla

A cewar Griezmann kyautar gwarzon dan wasan kwallon kafa na bana daga FIFA na tattare da nakasu, ganin cewa a cikin gwanaye ukun da ta ware, babu koda dan wasa guda da kasarsa ta lashe gasar cin kofin duniya a bana.

Sai dai a cewar Griezmann, ko ba komai yana sa ran lashe kyautar gwarzon dan wasan duniya ta Ballon d’Or da masu ruwa da tsaki kan kwallon kafa na Faransa ke bayarwa a duk shekara.

Giezmann ya kara da cewa yana da kwarin gwiwar yana gaban Ronaldo da Messi wajen cancantar lashe kyautar ta Ballon d’Or, la’akari da rawar da ya taka wajen nasarar da kungiyarsa ta Atletico ta samu wajen lashe gasar Europa a bana, da kuma lashe gasar cin kofin duniyar da kasarsa Faransa ta yi.

A ranar 24 ga watan Satumba, 2018, hukumar FIFA za ta mika kyautar karramawa ta gwarzon dan wasan kwallon kafa na duniya ga daya daga cikin ‘yan wasa uku da ta zabo, Cristiano Ronaldo, Luka Modric da kuma Muhammad Salah.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.