Wasanni

Ronaldo ya jefa kwallon farko a Juventus

Cristiano Ronaldo ya zura kwallonsa ta farko a gasar Serie A ta Italiya tun bayan da ya koma Juventus daga Real Madrid
Cristiano Ronaldo ya zura kwallonsa ta farko a gasar Serie A ta Italiya tun bayan da ya koma Juventus daga Real Madrid REUTERS/Massimo Pinca

Christiano Ronaldo ya jefa kwallayensa na farko a raga tun bayan da ya koma Juventus don ci gaba da murza leda daga Real Madrid.

Talla

Dan wasan ya zura kwallaye biyu a fafatawar da Juventus ta doke Sassuolo da ci 2-1 a gasar Seria A bayan da ya buga wa kungiyarsa tasa wasanni uku ba tare da jefa kwallo ba.

Kiris ya rage dan wasan mai shekaru 33 ya jefa kwallaye fiye da biyu a fafatawar ta jiya, lura da cewa ya barar da damammakin zura kwallo har guda biyu da ya samu.

A bangare guda, alkalin wasa ya yi waje da dan wasan Juventus, Douglas Costa bayan fasahar bidiyon da ke taimakawa alakalin ya nuna shi yana tofa wa Federico di Francesco yawu bayan takaddamar karbe kwallo da ta kaure a tsakaninsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.