Wasanni

Bama tsoron haduwa da kowace kungiya - Liverpool

Mai horar da kungiyar Liverpool Juergen Klopp, tare da wasu 'yan wasansa.
Mai horar da kungiyar Liverpool Juergen Klopp, tare da wasu 'yan wasansa. REUTERS/Andrew Yates

Mai horar da kungiyar Liverpool Jurgen Klopp, ya ce ‘yan wasansa basa tsoron haduwa da kowace kungiya a gasar cin kofin zakarun nahiyar turai.

Talla

Klopp ya yi wannan ikirarin ne bayan kammala wasan farko da suka fafata na gasar zakarun nahiyar turai ta bana a filin wasansu na Anfield, inda suka samu nasara akan kungiyar Paris Saint Germain da kwallaye 3-2.

Mai horar da kungiyar ta Liverpool dai na kallon wasan na ranar Talata, 18 ga Satumba na 2018, a matsayin kakkarfan tubalin da suka kafa a gasar zakarun turai ta bana, bayan irin nasarar da suka samu ta zuwa matakin wasan karshe a gasar da ta gabata, inda suka yi rashin nasara a wasan.

A matakin wasannin gasar Premier ta Ingila ma dai, kungiyar ta Liverpool na taka rawar gani, inda ta lashe dukkanin wasanni biyar da ta buga.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.