Wasanni

Costa ba zai bugawa Juventus wasanni hudu ba

Hukumar kula da wasannin kasar Italiya, ta haramtawa dan wasan gaba na Juventus Douglas Costa buga wasanni 4, sakamakon laifin da ya aikata na tofawa dan wasan kungiyar Sassuolo Federico Di Francesco yawu a fuska.

Douglas Costa na Juventus, a lokacin da alkalin wasa ya bashi jan kati, sakamakon tofawa dan wasan kungiyar Sassuolo Di Francesco yawu a fuska.
Douglas Costa na Juventus, a lokacin da alkalin wasa ya bashi jan kati, sakamakon tofawa dan wasan kungiyar Sassuolo Di Francesco yawu a fuska. REUTERS/Massimo Pinca
Talla

Costa ya tofawa Di Francesco yawun a fuskarsa ne, yayinda suke fafata wasan gasar Seria A a karshen makon da ya gabata.

Bayan sanar da yanke hukuncin, mai horar da Juventus Massimiliano Allegri ya ce kungiyar ba za ta daukaka karar neman sokewa ko rage tsaurin hukuncin da aka yanke kan dan wasan nata ba.

Sai dai duk da haka Douglas Costa na cikin tawagar Juventus da za ta fafata da kungiyar Valencia a yau Laraba a wasan farko da kungiyoyin za su buga na gasar cin kofin zakarun nahiyar Turai.

Koda ya ke Costa ya nemi afuwar, abokan wasansa da magoya baya a sakon da ya wallafa a shafinsa na Instagram, dan wasan ya ce mutane basu da masaniyar irin munin kalaman da Di Francesco ya furta masa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI