Wasanni

"Joshua na cin abincin da zai kosar da mutane 4 a rana guda"

Zakaran dan wasan Damben Boxing na duniya Anthony Joshua yayin lallasa Joseph Parker a Birtaniya. 31 ga watan Maris, 2018
Zakaran dan wasan Damben Boxing na duniya Anthony Joshua yayin lallasa Joseph Parker a Birtaniya. 31 ga watan Maris, 2018 Reuters/Andrew Couldridge

Wasu bayanai daga makusantan gwarzon dan damben boxing na duniya dan Birtaniya, Anthony Joshua, sun ce abincin da dan damben ke lakumewa a kowace rana guda, ya isa ya ciyar da lafiyayyun mutane hudu, a lokutan safiya, rana da kuma dare.

Talla

Rahoton da jaridar ‘The Sun’ ta wallafa, ya zo ne a yayinda Anthony Joshua, ke shirin kece raini da takwaransa Alexander Povetkin na Rasha, ranar Asabar mai zuwa a Ingila.

Kadan daga cikin irin abincin da shirgegen dan damben ke sharewa ya hada da kawi biyar a kowace safiya da kuma kirazan kaza guda biyu, amma fa manya da suka yi daidai da girman takwarorinsu matsakaita guda hudu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.