Wasanni

An kori Ronaldo daga filin wasan zakarun Turai

Cristiano Ronaldo
Cristiano Ronaldo REUTERS/Alberto Lingria

Christiano Ronaldo ya fice daga filin wasa cikin hawaye bayan alkalin wasa ya manna masa jan kati a fafatawar Juventus da Valencia a gasar cin kofin zakarun nahiyar Turai.

Talla

Alkalin wasan dan asalin Jamus, Felix Brych ya kori Ronaldo ne a minti na 29 da  fara karawar a Estadio Mestalla bayan ya yi cacar-baka da Jeison Murillo da ke tsaron bayan Valencia.

Murillo na bibiyar Ronaldo sau da kafa a wasan har ta kai ga gwarzon dan wasan ya kai masa duka a yayin da suke gwagwarmayar daukar kwallo.

Nan take Murillo ya fadi kasa, lamarin da ya ja hankalin alakalin wasa har ya gana da mataimakinsa kafin daga bisani ya dawo kan fili don nuna jan kati ga Ronaldo.

Yanzu haka dan wasan ba zai buga wasan da Juventus za ta yi a ranar 2 ga watan Oktoba ba da Young Boys a matakin rukuninsu na H.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI