Wasanni

Lionel Messi ya dawo da karsashinsa na kwallo

A karo na 48 kenan da Lionel Messi ke zura kwallaye uku-uku a jumullar wasannin da ya buga wa Barcelona
A karo na 48 kenan da Lionel Messi ke zura kwallaye uku-uku a jumullar wasannin da ya buga wa Barcelona REUTERS/Sergio Perez

Lionel Messi na Barcelona ya fara gasar zakarun Turai a bana da cikakken karsashi, lura da kwallaye uku da ya zazzaga a wasan da suka lallasa PSV Eindhoven da ci 4-0 a ranar Talata.

Talla

Bayan jefa kwallon ta uku, abokan wasansa sun rufe shi saboda murna, yayin da magoya bayansa suka yi ta wake-waken kiran sunansa, in da kuma kocinsa, ya bayyana shi a matsayin wani abu da ba a taba gani ba cikin tsawon shekaru.

A karo na takwas kenan da Messi ke zura kwallaye uku-uku a wasannin zakarun Turai, in da ya zarce babban abokin hamayyarsa na Juventus Christiano Ronaldo , wanda ya zura kwallaye uku-uku har sau bakwai a wasannin na gasar zakarun Turai.

Ana iya tuna wayadda Messi ya gaza kai tawagar kasarsa ta Argentina ga gaci a gasar cin kofin duniya a Rasha, yayin da Roma ta yi waje da su a gasar zakarun Turai a bara, abin da bisa dukkan alamu ya bakanta ran gwarzon dan wasan, musamman idan aka yi la'akari da jawabin da ya yi wa magoya bayansa a Camp Nou.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.