Wasanni

Modric ya tsira daga fuskantar hukuncin dauri

Luka Modric na kungiyar Real Madrid.
Luka Modric na kungiyar Real Madrid. REUTERS/Darren Staples

Dan wasan tsakiya na Real Madrid Luka Modric ya cimma yarjejeniya hukumomin Spain, bayan amincewar da yayi cewa ya aikata laifin kaucewa biyan haraji.

Talla

Sakamakon cimma yarjejeniyar, a halin yanzu Modric dan kasar Croatia, ba zai yi fuskanci daurin watanni 8 kamar yadda aka shirya da fari ba, inda za a sauya hukuncin zuwa biyan tara.

A watan Disamba na shekarar 2017 da ta gabata, hukumomin Spain suka zargi Modric mai shekaru 33 da kin biyan harajin euro dubu 870,728.

A halin yanzu Modric zai biya tarar akalla kashi 40 na yawan kudaden harajin da ya kaucewa biya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.