wasanni

Wa zai lashe kyautar gwarzon dan kwallon duniya?

Luka Modric da Cristiano Ronaldo da Mohamed Salah na fafatawa da juna wajen lashe kyautar gwarzon dan kwallon duniya a bana
Luka Modric da Cristiano Ronaldo da Mohamed Salah na fafatawa da juna wajen lashe kyautar gwarzon dan kwallon duniya a bana NewsATW

Wani lokaci a yau ne Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya, FIFA za ta gudanar da bikin karrama gwarzon dan wasan kwallon kafa na bana a birnin London.

Talla

Cristiano Ronaldo na Juventus da Luca Modric na Real Madrid da kuma Mohamed Salah na Liverpool na fafatawa da juna wajen lashe wannan gagarumar kyauta, in da a bana suka yi wa Lionel Messi zarra waanda ya gaza shiga sahun zaratan 'yan wasan a wannan karo.

Kazalika za a karrama ‘yar wasa mace da ta fi kwarewa wajen taka leda a bana da kuma masu horarwa har ma da bangaren masu tsaren reaga.

A bangaren mata akwai Ada Hegerberg ta Lyon kuma ‘yar asalin kasar Norway, sai kuma Dzsenifer Marozsan ta Jamus wadda ke taka leda a Lyon. Sai kuma Marta ‘yar asalin Brazil da ke buga kwallo a Orlando Pride.

Bangaren koci kuma akwai Zinedine Zidane da ya raba gari da Real Madrid da Didier Deschamp, mai horar da tawagar Faransa da kuma Zlatko Dalic da ke horar da tawagar Croatia.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.