wasanni

Gwarzon duniya: Modric ya kawo karshen Ronaldo da Messi

Gwarzon dan wasan shekara, Luka Modric da gwarzon kocin bana, Didier Deschamps da kuma gwarzuwar 'yar wasan shekara, Marta a wajen bikin da FIFA ta gudanar a London
Gwarzon dan wasan shekara, Luka Modric da gwarzon kocin bana, Didier Deschamps da kuma gwarzuwar 'yar wasan shekara, Marta a wajen bikin da FIFA ta gudanar a London Action Images via Reuters/John Sibley

Dan wasan Real Madrid Luca Modrci ya lashe kyautar Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya da take bai wa gwarzon dan kwallon duniya na shekara a wani biki da ya gudana a birnin London, abin da ya kawo karshen kane-kanen da Cristiano Ronaldo da Lionel Messi suka yi wajen lashe kyautar a tsakaninsu cikin tsawon shekaru.

Talla

Modric ya doke Ronaldo na Juventus da Mohamed Salah na Liverpool wajen lashe wannan gagarumar kyautar a bana.

Dan wasan mai shekaru 33 ya lashe kofin zakarun nahiyar Turai karo na uku a jere a kungiyarsa ta Real Madrid, sannan ya jagoranci kasarsa ta Croatia har zuwa matakin wasan karshe a gasar cin kofin duniya da aka gudanar a Rasha.

Ronaldo bai samu damar halartar bikin karramawar ba, yayin da har ila yau Mohamed Salah ya doke shi wajen lashe kyautar Puskas da ake bai wa dan wasan da ya jefa kwallo mafi kyawun ciyuwa a raga.

Ko da dai wasu na ci gaba da jinjina wa Ronaldo kan kwallon da ya jefa ragar Juventus a bara a gasar cin kofin zakarun nahiyar Turai, wadda ta kai ga magoya bayan Juventus a Turin mikewa tsaye don girmama shi.

Wani abu da ke ci gaba da dagula tunanin magoya bayan Salah shi ne yadda aka cire sunansa daga cikin jerin ‘yan wasan FIFA 11 da suka fi iya taka leda duk da cewa yana cikin ‘ya wasa 3 ta suka yi takarar lashe kyautar gwarzon dan wasan bana.

JERIN 'YAN WASAN FIFA 11 NA BANA

David de Gea ( Manchester United )

Dani Alves (Paris Saint-Germain)

Raphael Varane ( Real Madrid )

Sergio Ramos (Real Madrid)

Marcelo (Real Madrid)

Luka Modric (Real Madrid)

N'Golo Kante ( Chelsea )

Eden Hazard (Chelsea)

Lionel Messi ( Barcelona )

Kylian Mbappe (Paris Saint-Germain)

Cristiano Ronaldo ( Juventus )

A bangaren guda an zabi Kocin tawagar Faransa, Didier Deschamp a matsayin gwarzon mai horarwa na shekara, yayin da 'yar wasan Brazil da ke taka leda a Orlando Pride, watO Marta ta lashe kyautar ta FIFA a bangaren mata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.