wasanni

Ronaldo zai fafata da Manchester United a gasar Turai

Cristiano Ronaldo bayan samun jan kati a wasan Juventus da Valencia
Cristiano Ronaldo bayan samun jan kati a wasan Juventus da Valencia Sergio Perez

Cristiano Ronaldo zai shiga fafatawar da Juventus za ta yi da Manchester United a watan gobe a Gasar Cin Kofin Zakarun Nahiyar Turai bayan an haramta masa wasa guda sakamakon jan katin da aka manna masa.

Talla

Hukumar Kwallon Kafar Nahiyar Turai, UEFA ta haramta wa Ronaldo mai shekaru 33 buga wasan da Juventus za ta yi da Young Boys a ranar 2 ga watan Oktoba sakamakon wannan jan katin da aka ba shi a wasan da kungiyarsa ta yi nasara da kwallaye 2-0 akan Valencia a makon jiya.

Ronaldo ya samu katin ne bayan samun sa da laifin jan gashin dan wasan baya na Valencia Jeison Murillo, kuma a karon farko kenan da ake ba shi jan katin tun bayan soma taka ledarsa a gasar zakarun Turai.

A ranar 23 Juventus din za ta ziyarci Old Trafford don kece raini da Manchester United.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.