Wasanni

Sevilla ta lallasa Real Madrid, Barcelona ta sha kaye a hannun Laganes

Cikin wani yanayi na bazata, Real Madrid ta kashi da kwallaye 3-0, a wasan gasar La liga da ta fafata kungiyar Sevilla a ranar Larabar nan.

Dan wasan gaba na kungiyar Real Madrid Karim Benzema, yayinda yake kokarin kurdawa tsakanin 'yan baya na Sevilla.
Dan wasan gaba na kungiyar Real Madrid Karim Benzema, yayinda yake kokarin kurdawa tsakanin 'yan baya na Sevilla. Reuters
Talla

Karo na farko kenan tun bayan shekarar 2003, da Real Madrid ta fuskanci irin wannan kaye na jefa mata kwallaye 3 kafin tafiya hutun rabin lokaci, a waccan lokacin shi ma kayen a hannun kungiyar ta Sevilla.

Wasan na jiya dai dama ce ga Real Madrid wajen darewa saman teburin gasar La liga, la’akari da rashin nasarar abokiyar hamayyarta Barcelona, wadda kungiyar Leganes ta samu nasarar akanta da kwallaye 2-1.

Sauran wasannin gasar La Liga da aka buga a jiya sun hada da, wasan da Villarreal ta samu nasara kan Athletic Bilbao da kwallaye 3-0, sai kuma wasa tsakanin Valencia da Celta Vigo, wanda aka tashi kunnen doki, wato 1-1

Har yanzu dai Barcelona ke jagorantar gasar ta La liga da maki 13, yayinda Real Madrid ke biye mata, itama da maki 13, sai kuma Atletico Madrid da maki 11 a matsayi na uku.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI